1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana dab da kawar da zazzabin cizon sauro a Afirka

Abdourahamane Hassane
November 24, 2023

Nan ba da jimawa ba ne za a fara allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a yankunan da ke da hatsarin gaske a Nahiyar Afirka,

https://p.dw.com/p/4ZPMl
Hoto: Soumyabrata Roy/NurPhoto/picture alliance

 Hukumar dake kula da aiwatarda riga kafin (Gavi) ta ce yanzu haka dubban darurruwan alluran rigakafin na RTS,S, sun isa a Kamaru Alluran rigakafin na RTSS na zazzabin cinzo sauron wanda hukumar lafiya ta duniya OMS ta tabbatar da ingancinsu. wannan shi ne karo na farko da za a fara amfani da su. Hukumar riga kafin ta  GAVI ta ce kasahen Burkina Faso da Laberiya da Nijar da Saliyo ana sa ran za su sami allurai miliyan 1.7 na rigakafin  na RTS,S a cikin makonni masu zuwa. Yayin da wasu sauran kasashen Afirka za su samu a cikin watanni masu zuwa. A shekara ta 2021 mutane miliyan 247 suka kamu da cutar zazzabin cizon a duniya, yayin  da sama da dubu 600 suka mutu da cutar yawanci a kasahen kudu da hamada.