1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Kwango

Tattaunawar DW da Felix Tshisekedi

May 2, 2024

Watanni hudu bayan sake zabensa, shugaba Felix Tschisekedi na Jamhuriyar Demukaradiyyar Kwago na ziyara a Jamus da nufin karfafa hulda tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4fQkr
Felix Tshisekedi a hirarsa da tashar DW
Felix Tshisekedi a hirarsa da tashar DWHoto: DW

 Bude kofofiga abokan hulda na ketare don bukasa tattali arziki, da shawo kan matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa da kuma sarafa dumbin ma'adinan karkashin kasa da Allah ya huwace wa Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango don inganta rayuwar al'umma, kadan ne daga cikin alkawaran da shugaba Felix Tschisekedi ya dauka a lokacin da yake zawarcin kuri'un 'yan kasar domin samun wa'adin mulki a karo na biyu.

Watanni hudu bayan zuwansa kan gadon mulkin kasar da ke gabashi Afrika mai fama da manyan kalubale, Tschisekedi na kokarin tabbatar da wannan manufa ta hanyar shiga lungu da sako da nufin janyo hankali amintattun abokan hulda. A zantawa ta musamman da ya yi da DW, shugaba Tschikedi ya bayyana Jamus a matsayin kasar da ta dace domin kulla alaka mai aminci da ita a fannoni dabam-dabam na ci gaba musamman ma a kan makamashi, inda ya ce ya yi imani kasashen biyu za su  ribanta sosai.

Kwango na da tarin arizikin ma'adinai da duniya ke bukata

Videostill | Felix Tshisekedi im DW Interview
Hoto: DW

 ''Allah ya albarkaci Kwango da dumbin arziki. Abin da ya rage shi ne sallamowar masu saka hannu jari don sarrafa wadannan albarkatu. Fannin samar da  makamashi na a sahun farko na fannin da zan bukaci Jamus ta saka hannun jari domin a bunkasashi, kana daga bisani sai fannonin ilimi da kiwon lafiya da noma da ke da matukar mahimmanci a wannan lokaci. Baya ga haka sai kuma fannin sadarwa da kimiyar zamani da matasanmu suka fara raja'a a kai.''

Matsalar rashin tsaro da tawaye sun hana Kwango ci gaba

Sai dai matsalar tsaro mai nasaba da kungiyoyin masu dauke da makamai da kuma 'yan tawayen M23 masu samun goyoyon bayan Ruwanda da suka hana sukuni a yankunan kasar masu arzikin ma'adinai, na zama babban kalubale ga kasar. Ana ma fargabar wannan rikici ya haifar da barkewar yaki tsakanin DRC Kwango da makwabciyarta Ruwanta da suke wa juna kallon hadarin kaji. To amma a tambayi shugaba Tschisekedi ko zai gana nan zuwa gaba da takwaransa   Paul Kagamedon warware wannan dambarwa?