1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta kashe trilliyan 12 wajen shigo da abinci

May 3, 2024

A shekaru takwas na tsohuwar gwamnati Buhari sama da Naira trilliyan daya ne babban bankin kasar na CBN ya kashe a kokarin samar da isashen abinci.

https://p.dw.com/p/4fROI
Hoto: Ubale Musa/DW

Bayan share shekaru a kokarin tarayyar Najeriya na kai gaci bisa batu na abinci , daga dukka na alamu har yanzu kasar na kashe makudan kudi cikin batun mai tasiri. Kama daga   shinkafazuwa ga alkama da ma raguwa na bukatu na abincin dai Najeriyar tai ikirarin kai wa zuwa gaci cikin batun na abinci har yanzu da  saura.

Najeriyar na bukatar akalla tan miliyan biyar na abinci domin amfanin miliyoyi na 'yan kasar 

Nigeria Reis-Pyramide gegen den Hungersnot im Land
Hoto: Ubale Musa/DW

To sai dai kuma a yayin da masu mulki na kasar ke buga kirjin kai wa ga cigaba, wata sabuwar kiddidiga na cewar kasar ta kashe trilliyan dai-dai har   12wajen shigo da abincin da ke zaman mai tasiri. Duk da karuwa ta noman shinkafa dai , kiddididgar ta hukumar kiddidgar tarayyar Najeriyar dai ta kuma ce kasar ta kalli karuwar shigo da alkama da manja da kifi dama raguwa na bukatun na ci da kai da ke zaman babban kwazo. Tuni dai dama batun tsaro da ma yawan al'umma ya zamo barazana ga masu mulki na kasar da suka kalli hauhawa ta farashi na abincin, da ta yi barazanar komawa rikici mai girma. Yanzu haka Najeriyar na bukatar akalla tan miliyan biyar na abinci domin amfanin   miliyoyi na 'yan kasar.