1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Switzerland ta daure tsohon ministan Gambiya

Abdul-raheem Hassan
May 15, 2024

Tsohon jami'in a gwamnatin kasar Gambiya Ousman Sonko, na fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari bisa laifin cin zarafi a mulkin Yahya Jammeh. Za a hana tsohon ministan shiga Switzerland tsawon shekaru 12.

https://p.dw.com/p/4ftmq
Hoto: fikmik/YAY Images/IMAGO

Kotun hukunta man'yan laifuka ta kasar Switzerland, ta yanke wa tsohon ministan cikin gida na kasar Gambiya Ousman Sonko  hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari. An sami Sanko mai shekaru 55 da laifin cin zarafin bil adama a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh tsakanin shekarun 2000 zuwa 2016..

Kotun ta ce za kuma a haramta wa Ousman Sonko shiga kasar Switzerland na tsawon shekaru 12 da zarar an yanke hukuncin, sannan za a tilasta masa biyan diyya ga mutanen da ya azabtar.