1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Benin ta dauki mataki kan Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
May 7, 2024

Gwamnatin Jamhuriyar Benin, ta dauki matakin haramta wa Jamhuriyar Nijar sayar da danyen man fetur dinta a kasuwar duniya daga runbun ajiyar danyen man da ke tashar jiragen ruwa ta Seme a birnin Cotonou.

https://p.dw.com/p/4fanM
Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin da Janar Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin da Janar Abdourahamane Tiani na Jamhuriyar NijarHoto: Yanick Folly/AFP/Getty Images, ORTN/TÈlÈ Sahel/AFP

Wannan matakin dai ya fara haifar da muhawara a tsakanin 'yan Nijar din, a yayin da wasu ke nuna bacin ransu da matakin hukumomin Benin din wasu kuma ke ganin dacewar hakan. Rahotanni daga Benin na nunar da cewa Shugaba Patrice Talon ne da kansa ya dauki matakin haramta loda man ga duk wani jirgin dakon man da ya zo daukar danyen man wanda Nijar ta sayar a kasuwar duniya, daga runbun ajiyar danyen man nata da ta gina a tashar ruwan Seme ta gabar ruwan Cotonou tare da sanya sharadin ga Jamhuriyar ta Nijar, bayan da ta ci gaba da rufe kan iyakarta duk da dage mata takunkumi da ECOWAS ko CEDEAO ta yi. 

Tashar jiragen ruwan Cotonou na Jamhuriyar Benin
Tashar jiragen ruwan Cotonou na Jamhuriyar BeninHoto: AP

Kilomita sama da 2000 ne na bututun man dai Chaina ta gina wa Nijar daga yankin Agadem, inda take hakar mai zuwa tashar ruwan Cotonou domin sayar da shi kai tsaye a kasuwanni duniya. Shirin da hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar ke dogaro da shi wajen samar da kudin shiga na tafiyar da ayyukan gina kasa. Tuni dai hukumomin mulkin sojan Nijar din suka jinginar da man da za ta hako a tsawon shekara guda ta farko ga kasar Chaina, tare da karbar bashin kudi dalar Amurka miliyan 400. Sai dai kuma sabuwar kungiyar tawayen Nijar ta FPL ta bai wa Chainan wa'adin mako guda na ta soke yarjejeniyar bashin da ta bai wa Nijar din, ko kuma ta soma kaddamar da hare-hare a kan kamfanin hakar man na Agadem da sauran kadarorinsa.