1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Cece kuce kan dokar auren jinsi a Iraki

April 30, 2024

Matakin da majalisar dokokin Iraqi ta dauka na gyaran fuska a dokar aure da soyayya tsakanin jinsi daya na ci gaba da jawo cece kuce da takaddama a ciki da wajen kasar

https://p.dw.com/p/4fN8O
Irak Schweden Protest Moqtada Sadr
Hoto: Hadi Mizban/AP/picture alliance

'Yan majalisar dokoki sun kada kuri'a kan sabuwar dokar haramta aure da soyayyar jinsi a kasar ta Iraki, dokar da majalisar ta ce ta yi la'akari da tarin koke koken da aka yi ta yi a baya kan auren jinsi, kafin yi mata kwaskwarima da amincewa da ita, kamar yadda kakakin majalisar Haidary Isma'ily ya baiyana.

 "An soke tsohuwar dokar da ke haramta karuwanci kadai a Iraki, an maye gurbinta da dokar da ke haramta karuwanci da alakar jinsi, dama duk wasu matakan tallatasu ko goyon bayansu da bayyanasu a bainar jama'a. Wannan sabuwar doka ce da ta yi sasauci ga masu alakar jinsi, wadanda ada ake yanke musu hukuncin kisa, yanzu hukuncin zai takaita ne ga daurin da ya kama daga shekaru 10 zuwa 15, don dakile alakar jinsi a Iraki."

'Yan majalisar dokokin Iraqi a Bagadaza yayin kada kuri'a kan kudirin doka
'Yan majalisar dokokin Iraqi a Bagadaza yayin kada kuri'a kan kudirin dokaHoto: IRAQI PARLIAMENT MEDIA OFFICE/REUTERS

Karkashin sabuwar dokar, masu goyon bayan luwaɗi da maɗigo da kuma karuwanci za su fuskanci hukuncin ɗauri, mafi ƙaranci shekaru 7 a gidan yari, yayin da ƴan daudu ke fuskantar ɗaurin shekara ɗaya zuwa uku. Za a yanke wa masu sauya jinsi hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari. Kazalika likitocin da ke yin tiyatar sauya jinsi ga masu buƙata, za su fuskanci hukucin da zai kai shekaru uku a gidan yari.

 Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka yi Allah wadai da wannan dokar da suka ce,za ta danne wa miliyoyin 'yan kasar hakkin tsarin rayuwarsu da biyan bukatunsu na bil Adama da suka zaba wa kansu.

Ra'id Hulwani shine shugaban haramtacciyar kungiyar yan Daudun kasar ta Iraki da aka sako watanni shida da suka gabata, bayan da ya gama zaman jarum na shekara guda kan laifin yada badala a bayan kasa:

Firaministan Iraqi Mohammed Shia' al-Sudani
Firaministan Iraqi Mohammed Shia' al-SudaniHoto: Iraqi Parliament Media Office/AP/picture alliance

 "Amincewar majalisa da wannan dokar babban cin zali ne ga yan luwadi da madigo, wadanda dabi'ar jikinsu ta saba da ta sauran mutane. Mene ne laifinsu? don sun biya bukatun jikinsu ta hanyoyin da basu yi wa sauran mutane dadi ba?.A madadin hukuma ta karesu daga cin zarafi da tsangwama da kashe su da ake yi, abin takaici ne a ce za a sanya wannan azzulumar dokar da ke danne musu hakkokinsu na rayuwa."

 A hannu guda, galibin 'yan kasar ta Iraqi da ke goyon bayan wannan dokar da suka dauka a matsayin kandagarki ga miyagun al'adun da ke shigowa kasar daga ketare, wadanda kuma suke kokarin mayar da mutane tamkar dabbobi, suna nuna fargabar cewa,sassaucin da aka yi a dokar daga hukuncin kisa zuwa dauri kadai, kan iya share fagen soke dokar baki daya, sakamakon matsin lambar kasashen ketare, kamar yadda ya faru a wasu kasashe da dama.

  "Ina goyan bayan wannan doka duk da dari darin da nake da sassaucin da aka yi a cikinta. Domin mu a nan kasar Iraqi, ba a barinmu mu tsara wa kanmu dokoki da tsarin mulki da na zamantakewa ba tare da an yi mana katsalandam daga ketare ba. Fatanmu mahukunta su aiwatar da wannan dokar ba sani ba sabo."

Masu rajin kare 'yancin masu neman Jinsi
Masu rajin kare 'yancin masu neman Jinsi Hoto: Hassan Ammar/AP/picture alliance

A hannu guda, kwamatin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya yayi zama kan wannan dokar ta Iraqi, yadda ya caccaki dokar da yace ta saba wa tafarkin dimukuradiya da hakkin bil Adama a kasar ta Iraki da ke da mabanbanta kabilu da adidinai.

An dai yi ta samun kasashen da suka haramta alakar jinsi a 'yan shekarun nan a kasashe masu tasowa, amma sai akan Iraki ne kwamatin na Majalisar Dinkin Duniya ke yin zama kanta, lamarin da ke dasa ayar tambaya da fargaba ga yan kasar ta Iraqi da kudirorin Majalisar Dinkin Duniya a baya suka yi sanadiyar daidaita kasar.