1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Amincewa da yankin Falasdinu bisa manufa

May 10, 2024

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da gagarumin rinjaye ga yankin Falasdinu a matsayin cikakkiyar mamba a bisa manufa a zauren.

https://p.dw.com/p/4fjCr
Babban zaure MDD ya amince da kasancewar Falasdinu a matsayin mamba bisa manufa
Babban zaure MDD ya amince da kasancewar Falasdinu a matsayin mamba bisa manufaHoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

Kasashe mambobin Majalisar 143 ne suka kada kuri'ar amince wa da kara daukaka darajar Falasdinu yayin da wasu tara suka kada kuri'ar kin amincewa baya ga wasu 25 da suka kaurace wa kada kuri'a. Kudurin ya kara bayar da dama ga karin rawar da Falasdinawa za su taka a zauren, tare da yin kira ga kwamittin sulhu na Majalisar ya amince da Falasdinun ta zama cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya. 

Karin bayani: Falasdinu na son dauketa a matsayin kasa

Yayin da take mayar da martani, ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta ce, kuri'ar da zauren ya kada ya nuna cewa sun cacanci zama cikakkun mamba.