1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin Alluran Rigakafi a Ghana

March 29, 2023

'Yan kasar Ghana na kokawa kan yadda suke fuskantar matsalar karancin magungunan rigakafi, da ake yi wa kananan yara lokaci zuwa lokaci

https://p.dw.com/p/4PS0l
Malaria-Bekämpfung in Afrika | Kenia | Impfstoff Mosquirix
Hoto: Brian ONGORO/AFP

A watannin da suka gabata ba a samun magunguna ba saboda karancin su. Rashin mangungunan dai na kawo cututtukan da galibi kan addabi kananan yaran a Ghana. 
Kasar ta Ghana dai na fuskantar durkushewar harkokin tattalin arziki, wanda hakan ya shafi fannin kula da lafiya, inda asibitoci da dama ke samun karancin magunguna, da wadanda suke na rigakafi. Wannan matsalar dai na kara dagulewa ne sakamakon tashin farashin Dalar Amurka a kan kudin kasar wato Cedi. 
Kungiyoyin agaji da suka saba bayar da tallafi sun nade hannayensu musamman yadda kasar ke cikin jerin kasashe masu samun matsakaicin kudaden shiga. Kungiyar likitocin kasar ta Ghana ta yi gargadin cewa karancin magungunan na iya haifar da mummunan yanayi ga lafiyar kananan yara. A asibitin da ke yankin yammacin Tamale, ana iya ganin kamar komai na tafiya daidai, amma ba haka abin yake ba, saboda babu abin da ke tafiya ko samuwa da sauki, saboda yaran da ke cikin dakunan kula da majinyata na fama da cutar shan inna, inda aka kebe su a wani daki na musammam saboda kare sauran yara daga kamuwa da cutar. Abiba Mohammed na daya daga cikin iyaye da 'yarta ke fama da wannan cuta ta shan inna, ta kuma bayyana cewa rashin allurar rigakafi ne ya janyo wa 'yar tata wannan matsalar da take ciki a yanzu.

Allurar rigakafi ga yara kanana
Hoto: Brian ONGORO/AFP

"Idan da an yi wa 'yata allurar rigakafi da za ta kare ta daga kamuwa da cutar kyanda, to da ba ta kamu da wannan cuta ba. Yara da dama ba a yi musu allurar ba saboda karancin mangani, abin da ya jawo matsalar da muke ciki kenan a yanzu." 

Watanni shida kenan, da wuraren kula lafiya ke fama da wannan matsalar ta karancin magungunan rigakafi na yara kamar yadda guda daga cikin jami'an kiwon lafiyar ta bayyana. 

WHO Malawi Malaria Impfstoff
Hoto: Jerome Delay/AP Photo/picture alliance

"Tun daga haihuwa zuwa makwanni 14, ba mu da magani. Kamar na cutar shan inna, wanda ake ba da allurarta daga haihuwa, ita ma ba mu da maganin a yanzu. Na kwayar cutar Rotavirus ma ba mu da magani, har ma da na kyanda, duk babu su."
 
Akwai iyaye mata da suka shafe watanni suna ziyartar asibitoci saboda su yi wa yaransu allurar rigakafin amma, duk kokarin su ya ci tura. A can baya dai tattalin arzikin kasar Ghana ya bunkasa, wanda ya sa bankin duniya ya sanya ta a matsayin kasa mai matsakaicin kudin shiga. Domin hakan ya sa masu tallafa wa kasar suka daina ba ta gudumawa, har ma ga fannin lafiya. A daya hannun ma gwamnatin ta so ta kawar da yawan dogaro da take yi da masu tallafa mata, amma saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar a halin yanzu, ya sa take fadi tashi a bangaren neman shawo kan matsalar allurar rigakafin cuttukan yara. Awal Ahmed Kariyama, mai fafutuka ne ta fannin kula da lafiya, ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta ajiye girman kanta ta nemi taimakon kasashen ketare. 

Hoto: Brian Ongoro/AFP

"Lokaci ne da gwamnati za ta mika wuya, duk da cewa muna son ganin Ghana ta wuce matsayin neman agaji, ko da yake kasarmu na cikin kasashen da ke da matsakaicin kudin shiga, amma akwai wasu abubuwa da ya kamata a magance su tare da yin kira da neman goyon bayan da za mu iya samu daga dukkan abokan hulda."
 
A cewar Baraimah Baba Abubukari darakta a fannin kula da lafiya, Ghana ta kasance tana da kyakkyawan tarihin bai wa allurar rigakafi muhimmanci da kusan kashi 95%, amma ma'aikatar lafiya ta bayyana cewa wannan ƙarancin alluran na haifar da matsaloli ga yara.  

"Idan ba a yi wa yaranmu rigakafi ba, akwai wasu cututtuka da garkuwar jikinsu ba za su iya yin yaki da su ba don haka idan suka ci karo da su sai kuma cuttukan su samu galaba a kan lafiyar wadannan yara inda a karshe suke iya zama masu tsananin gaske."

A matsayin mataki na gaggawa dai gwamnati kasar Ghana ta kawo wasu alluran rigakafi daga Najeriya, yayin da take jiran karbar nata rigakafin. Amma kwarraru sun ce hakan ba zai isa ba saboda adadin yawan bukatar da ake da ita yanzu a kasar.